Kuji Tsoron Allah ku Saukakawa Al’umma Ko Annabi S A W Yayi Alfahari Daku – Shugaban Hukumar Shari’a Ga Yan Kasuwa

IMG 20250216 182808

Shugaban hukumar Shari’a ta jihar Kano Malam Abbas Abubakar Daneji yayi kira ga yan kasuwa da su ji tsoron Allah su yi koyi da kiran shugaba S A W na Saukakawa masu siya ko a dace da rahamar Allah.

Shugaban yayi wannan kiran ne yayin wata ziyarar aiki da shi da kwamishinoninsa na daya a hukumar Gwani Hadi da kwamishina na biyu Malam Ali Dan Abba da sauran daractocinsa da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar su ka kai gidan da Hukumar ta waje domin kula da wadanda suka baro garuruwansu suka zo Kano aka musuluntar dasu.

An tanadar da wadannan gidajen ne a unguwar Gwale Da Sallari, wanda sama da mutane 50 ne a cikin wadannan gidajen wanda hukumar ke dawainiya da su da kuma bayin Allah daga cikin birnin Kano.

Malam Ali Dan Abba ya umarce su da su zama jakadun kirki a ko ina suke, domin Addinin Musulunci addini ne na mutanen kirki kuma masu tsafta a ko ina suke, kuma ya tabbatar musu da cewar gwamnatin Kano zata kara zage damtse wajen kulawa da karatunsu da Lafiyarsu da sauran dawainiyarsu ta yau da kullum.

Shima gwani Hadi ya kara da yi musu nasihar kara jajircewa duk da irin kalubalen da zai riskesu, kuma yayi musu addu’ar Allah ya yi musu albarka yadda suna ji suna gani suka bar garuruwansu da iyayensu da iyalansu don su karbi kalmar Allah.

Hukumar Shari’a hukumace da aka samar da ita domin kulawa da duk wani sha’ani da ya shafi addini a jihar Kano a kowace irin mu’anula, da fatan gwamnan Kano zai dubi wannan hukuma kamar yadda ya zabo mata zakakuran shugabanni, to ya basu damar yin aikin da ya dace da farfaɗo da ita ta dawo hayyacinta, duba da yadda wasu shugabannin da suka gabata su yi mata kanshin mutu.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *