kungiyar Unique Child Education & Women Empowerment Association Ta Tallafawa Wata Islamiyya Da Kayan Koyo Da Koyarwa A Kano

Alfijir

Alfijir

Alfijir ta rawaito, kungiyar Unique Child Education and Women Empowerment Association (UCEAWEA) ta kai tallafin kayan karatu da na rubutu ga wata makarantr islamiyya ta matan aure da yara wato KHAIRUL HISAN ISLAMIYYA dake Unguwar Mariri Danladi Nasidi a garin kano.

Alfijir

Kungiyar ta yi wannan gagarumin aikin alherin ne kamar yadda ta saba a ire iren ayyukanta da ta ke gudanarwa duk shekarar a fadin jihar ta Kano 

A tattaunawar jaridar Alfijir da sakataren kungiyar Camarade Hassan Adamu Danguguwa ya bayyana mana cewar, wannan shine tallafi na farko da suka fara bawa wannan makarantar cikin wannan sabuwar shekarar 2022 kamar yanda suke gudanar da ire iren wannan ayyuka sau 3 a duk shekara.

Ya kara da cewar sun zagaya makarantar shi da membobinsa domin gani da ido in da suka tabbatar da cewa makarantar na da bukatar kujerun zama na dalibai, wanda shima za suyi iya yin su don ganin sun share musu hawayensu a ayyukan kungiyar na gaba.

Secretary din yayi kira ga shugabanni da masu hannu da shuni da su taimakawa kungiyar bi sa irin kokarinta na tallafawa harkar koyo da koyarwa da sauran cigaban matasa a fadin jihar Kano. 

Domin taba alli da kungiyar ga lamba nan da mail. 

+2348099669964 

uceweaorg@gmail.com

 A nata bangaren shugabar makarantar Khairul Hisan da ke unguwar Mariri a birnin Kano Malama, ta bayyana godiyarta ga Allah (SWA) da kuma kungiyar Unique Child Education and Women Empowerment Association (UCEAWEA) bisa wannan namijin kokarin da tayi na tallafin da ta basu na kayan koyo da koyarwa, sannan kuma ta kara da kura ga gwamnati da sauran kungiyoyin jihar da suyi koyi da ayyukan alheri da wannan kungiyar ke wanzarwa a fadin jihar kano

Sannan ta yi kira da sauran kungiyoyi da ke fadin jihar Kano da masu hannu da shuni, da su kawo musu dauki wajen karasa ajujuwan da suka fara ginawa suka tsaya don cigaban ilimi a jihar nan

Slide Up
x