Tsohon daraktan DSS Ya Magantu Akan Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa

IMG 20240211 125838

Tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mista Mike Ejiofor, ya bayyana cewa, tunaninsa na ƙin biyan kuɗin fansa na garkuwa da mutane ya canja bayan da a ka sace shi.

Alfijir labarai ta rawaito Mike ya yi watsi da batun biyan kuɗin fansa, ya jaddada cewa taɓarɓarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan ne ya sa mutane shiga harkar garkuwa da mutane a matsayin wata hanyar samun kuɗin shiga.

Ejiofor ya amince da damuwar da ake samu game da ƙaruwar satar mutane tare da jaddada buƙatar samar da hanyoyin da za a bi don magance matsalar.

Ya ba da shawarar cewa ba lallai a kau da matsalar bakiɗaya ba, amma tana buqatar a tura isassun kayan aiki, tare da mai da hankali kan sa ido sosai don tabbatar da an yi amfani da kuɗaɗen da aka ware domin tsaro yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana muhimmancin hana almubazzaranci da salon rayuwa a tsakanin shugabannin hukumomin tsaro, inda ya nuna cewa ya kamata a karkatar da kuɗaɗen wajen magance matsalolin rashin tsaro a maimakon son kai.

Ejiofor ya kammala da cewa, tavarvarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan na taimakawa wajen yawaitar garkuwa da mutane kamar yadda daidaikun mutane ke ɗauka a matsayin sana’ar samun riba a cikin wahalhalun da ake fama da su.

Ya jaddada gaggawar magance ƙalubalen tattalin arziki a matsayin wani vangare na hanyoyin da za a magance ayyukan aikata laifuka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *