Alfijr ta rawaito Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nesanta kansa daga taron tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa na Arewa Suka shirya
Alfijr Labarai
Kungiyoyin da suka shirya wannan taron sun hada da Arewa Consultative Forum, Arewa House, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum da Arewa Research and Development Project.
A wata wasika mai dauke da sa hannun mai magana da yawun yakin neman zabensa,
Abdulmumin Jibrin ne ya aikewa wadanda suka shirya taron hadin gwiwar, Kwankwaso ya bayyana cewa tuni ya shirya gudanar da yakin neman zabe a ranar, kuma tawagarsa na ci gaba da aiki da takardar manufofinsa, wanda aka yi alkawari a kai tun daga tushe.
Kwankwaso ya yi zargin cewa tawagarsa na da sahihan bayanai da ke nuna cewa an yi sulhu da wasu mutane da ke da hannu a cikin wannan yarjejeniya, kuma za a yi amfani da taron ne wajen nuna goyon baya ga wani dan takara daga Arewacin Najeriya.
Alfijr Labarai
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna da sahihan bayanai a hannunmu da ke nuna cewa an yi wa wasu mutane rangwame, kuma wadannan mutane sun kammala shirin mayar da taron ya zama dandalin amincewa ga wani dan takara.
“Mun yi imanin cewa, ba daidai ba ne kowace kungiya ta yi shirin amincewa da duk wani dan takara da sunan Arewa, musamman idan muna da ‘yan takara fiye da daya daga yankinmu.”
Ya kuma yi zargin cewa an dage taron ne daga ranar da aka fara shirya gudanar da taron domin ya zo daidai da taron dan takarar a jihar Kaduna.
“Mun lura cewa ranar da ta gabata ma an dage ranar kuma an kayyade sabuwar ranar da za ta yi daidai da ranar da za a gudanar da gangamin daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a Kaduna. Wannan ya kara tabbatar da bayanan da ke hannunmu cewa dan takarar ne ke daukar nauyin taron,” in ji sanarwar.
Alfijr Labarai
Don haka Kwankwaso ya gargadi masu shirya taron da su guji amincewa da duk wani dan takara domin hakan zai kara dagula al’amuran Arewa.
A cikin shirin zaman na tattaunawa, Kwankwaso zai yi jawabi ne a ranar Litinin, tare da Bola Tinubu na jam’iyyar APC da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), yayin da Atiku Abubakar na PDP ya yi jawabi a ranar Lahadi a waje taron.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Daily Trust