Labari Mai Dadi: Gobara ta tashi a jirgin ruwan Amurka na dakon jiragen sama na yaƙi mai suna Gerald R Ford

IMG 230158 17326 1773784929707

Wata gobara ta tashi a jirgin ruwan Amurka na dakon jiragen sama na yaƙi mai suna Gerald R Ford yayin da yake aiki a Gabas ta Tsakiya a wani ɓangare na yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ta sa jami’ai fiye da 600 sun rasa gadaje , in ji wani rahoto da jaridar New York Times ta ruwaito.

Gobarar ta tashi ne a ɗakin wanki na jirgin ruwan a makon jiya, kuma jami’an soji sun ce ma’aikatan jirgin sun shafe sa’o’i 30 kafin su iya kashe ta.

Gomman jami’ai ne aka ba da rahoton cewa sun gamu da iftila’in shaƙar hayaƙi kuma biyu daga cikinsu sun samu kulawa sakamakon jin ciwo.

Jami’an jirgin da suka rasa gadajensu suna kwana ne a ƙasa da kan tebura, kuma tun da wutar ta samo asali ne daga ɗakin wanki, sojoji masu tuƙin jirgin ruwa ba su da yadda za su wanke kayayyakinsu.

TRT Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *