Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Yabawa Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da safiyo bisa Tallafawa Kungiyoyin al’umma da ke jihar Kano kayan Abinci don kara rage radadin rayuwa da kuɗin cefane 20k da Kowa da kowa a jiya Litinin da kuma yau Talata.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mai ba shi Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Hamza Buhari, ya bayyana haka a yayin rabon kayan abinci da Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, ya shirya domin tallafawa kungiyoyin al’umma da ke jihar Kano.
Ya kuma yaba kokarin Kwamishinan kan ayyukan alkhairi da yake gudanarwa, yana mai jaddada cewa irin wadannan shirye-shirye na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma. Ya kuma tabbatar da cewa zuwa ranar Talata, an raba kayan abinci da kudade da jimillar su ta kai sama da Naira miliyan 42.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka gudanar da taron na rana ta biyu, inda aka raba kayan abinci da kudade ga kungiyoyin al’umma da na jam’iyya domin tallafa musu.
Taron ya samu halartar Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, tare da wasu Kwamishinoni, masu bai wa Gwamna shawara, shugabannin sassan gwamnati, da kuma masu shirya fina-finan Hausa.
A yau kuma kungiyoyin da suka sami wannan tallafin buhun shinkafa 100 da taliya 100 da kuɗin cefane dubu ashirin ashirin sun haɗa da
1. Kungiyar APC Media Forum
2. Kungiyar APC Marshalls
3. Ƙungiyar APC Youth & Women
4. Kungiyar Kano First Movement
5. Ƙungiyar Abba Door to Door
6. Ƙungiyar Kannywood
Allah ya saka gwamna da wazirinsa Kwamishinan Kasa da safiyo ameen summa ameen




Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t