Labari Mai Dadi: Najeriya Za Ta Amfana da Dala Miliyan 5 Na MDD Don Magance Ambaliyar Ruwa

IMG 20250214 063032

Daga Aisha Salisu Ishaq

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ware dala miliyan biyar daga Asusun Gaggawa na Ƙasa (CERF) domin ɗaukar matakan rigakafi da rage illolin ambaliyar ruwa a Najeriya.

Wannan matakin na zuwa ne a matsayin amsa ga barazanar ambaliyar da ake hasashen za ta shafi yankunan arewacin Najeriya daga watan Yuni zuwa Yuli na shekarar nan ta 2025.

Mai tsara ayyukan jin kai na MDD a Najeriya, Mohamed Malick Fall, shi ne ya sanar da wannan shirin a ranar 12 ga Fabrairu, 2025 a Abuja, A cewar sa, “Yin tsammani da kuma ɗaukar matakin rigakafi kafin aukuwar matsala yana ceto rayuka, yana kuma rage hasarar abinci da kuma tasirin rashin lafiya.”

Yace Kudaden na CERF za su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati karkashin jagorancin ƙungiyar tsinkaya na gaba, wadda ke haɗa hukumomi kamar Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMET), Hukumar Ruwa ta Najeriya, da Hukumar Kula da Bala’o’i na Ƙasa, sannan aikin zai gudana ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Jin Kai na MDD (OCHA).

Ya kuma ce a watan Oktoban shekarar 2024 ne CERF ta fitar da dala miliyan 5 don rage illolin ambaliyar ruwa a jihohin Borno da Bauchi, da Sakkwato. inda wannan ya haɗu da dala miliyan 6 daga Asusun Jin Kai na Najeriya (NHF), aka kuma fitar da dala miliyan 2 don aikin tsinkaya, wanda ya taimaka wajen kare mutane kusan dubu dari 400,000 da ambaliyar ruwa ta shafa.

A wani rahoton NiMET na sheakrar 2025, ya nuna cewa ana hasashen cewa damina za ta faro ne a jihohin Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Sakkwato, Yobe, da Zamfara, wanda zai iya shafar amfanin gona da haifar da yunwa da yaduwar cututtuka kamar amai da gudawa.

Shirin na Jin Kai na Najeriya na 2025 ya ware kashi 5 cikin 100 na kasafin dala miliyan 910 don ayyukan rigakafi, amma wannan ya gaza biyan buƙatu. inda Rabon dala miliyan 5 daga CERF ya kai kashi 11 cikin 100 kacal na bukatun rigakafin. inda aka ce kuma ana kara bukatar ƙarin kuɗaɗe don ci gaba da ayyukan jin kai da rage illolin bala’o’i masu zuwa.

Daga nan sai Majalisar Ɗinkin Duniya tayi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su haɗa kai don ƙara tallafi da inganta shirye-shiryen tsinkaya na gaba domin kare rayuka da rage illolin ambaliyar ruwa a Najeriya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *