Labari Mai Dadi: Za’a Fara Kera Motoci Da Ababen Hawa A Kano.

FB IMG 1736500720196

Daga Aminu Bala Madobi

A karon farko, Gwamnatin jihar Kano ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfanin ƙasar China mai suna Kodong Manufacturing Nigeria Limited da zai riƙa harhada ababan hawa da suka hadar da motoci da babura masu aiki da batiri tare da samar da wuraren chajinsu a sassan jihar nan.

Da yake jawabi a yayin bikin sanya hannun, wanda aka gudanar a harabar kamfanin dake garin Dansudu a yankin karamar hukumar Tofa, Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya nanata kudirin gwamnatin jiha na ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin da zai karfafa gwiwar masu zuba jari a jihar nan.

Ya bayyana yarjejeniyar da cewa wata gagarumar nasara ce a yunkurin gwamnatin jihar Kano na ciyar da tattalin arzikin jihar nan gaba.

Mataimakin Gwamnan na Kano ya ce a irin wannan yunkuri ne gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cire duk wani takunkumi daga bangaren gwamnati da ya dabaibaye harkokin kasuwanci a jihar nan.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce idan kamfanin ya fara aiki gadan-gadan, zai samar da guraben aiki na kai tsaye kimanin dubu biyu da samar da karin dimbin ayyukan yi da ba na kai tsaye ba tare da bunkasa tattalin arzikin yankin da jihar Kano baki daya.
Ya ce gwamnati na sane da kalubalen da masu masana’antu ke fuskanta da suka hadar da kayan bukatu da hanyoyin isar da kaya zuwa kasuwa da ma kalubalen kudi.

Mataimakin Gwamnan ya nanata kudirin Gwamnatin jihar Kano na kiyaye dukkan sharuddan dake kunshin yarjejeniya domin samar da aminci a tsakanin juna.

Ya bukaci kamfanin da ya bayar da fifiko ga al’ummar garin Dansudu a yayin daukar ma’aikata manya da kanana.

Daga nan ya yi kira ga matasan da aka dauka aikin da ma wadanda za’a dauka su kasance masu gaskiya da amana tare da kiyayewa da kaidojin aiki.

Ibrahim Adam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *