Sanannen Daraktan finafinan masana’antar Kannywood, Malam Aminu Saira, ya koka game da halin taɓarɓarewar al’amura da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki musamman a shiyyar arewa.
Ya ce, al’ummar Arewa na buƙatar shugabanci na gari domin farfaɗowar harkokinsu na yau da kullum da a baya zalunci shugabanni ya yi sanadiyyar ɗaiɗaicewarsu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Malam Aminu Saira ya bayyana cewa al’ummar arewa ba su da ƙasar da ta fi Nijeriya, don haka sun cancanci samun rayuwa mai cike da ‘yanci da inganci kamar yadda kowane bil’adama yake samu a sauran ƙasashen duniya.
“Lokaci ya yi da za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe don kawar da azzalumai da kuma maƙiya arewacin Nijeriya. A saurari matakin farko da za mu fara shi a watan Afrilu”, inji daraktan.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma musamman masu rayuwa a jihohin arewacin Nijeriya suke fuskantar matsalolin rashin daidaiton al’amura da suka haɗa da tsaro da tattalin arziƙi duk da cewa shugabanci na gudana kamar yadda da shi a sauran sassan Afirka da na duniya baki ɗaya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t