Majalisar Dattawa ta titsiye shugaban JAMB domin ya yi bayanin yadda ya kashe miliyan 850 kan maganin ƙwari

FB IMG 1736797741692

Sanata Adams Oshiomhole na jam’iyyar APC wanda ke wakiltar Edo ta Arewa a yau Litinin ya tambayi Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) kan yadda ta kashe kudade a 2024.

Yayin da ya ke magana a wajen zaman kare kasafin kudin hukumar na 2025 a gaban Kwamitin Hada-Hadar Kudi na Majalisar Dokoki ta Kasa, Oshiomhole ya tambayi shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, da ya kare kashe Naira miliyan 850 kan harkokin tsaro, tsafta, da feshin maganin sauro a bara.

“Kun kashe Naira biliyan 1.1 kan abinci da kayan sha. Ana ba ku abinci kyauta ne daga gwamnati? Wannan yana nufin kuna kashe kudin da ku ka samu daga marasa galihu, da dama daga cikinsu marayu ne,” in ji shi.

“Har ila yau, kun kashe Naira miliyan 850 kan tsaro, share-share, da feshin maganin sauro a shekarar 2024. Me kuka feshe? Shin sauraye ne suka cinye wadannan kudi?”

Oshiomhole ya ci gaba da sukar JAMB kan kashe Naira miliyan 600 wajen tafiye-tafiye na cikin gida.

A nasa jawabin, Farfesa Oloyede ya bayyana cewa JAMB ta dawo da Naira biliyan 4 zuwa Asusun Hadakar Kudaden Gwamnati a 2024, yayin da ta samu tallafin Naira biliyan 6 daga Gwamnatin Tarayya.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *