Majalisar Dattawan Najeriya na Shirin Daƙile Shigo da Shinkafa Daga Ƙasashen Waje

IMG 224335 281025 1761687845705

Majalisar Dattawan Najeriya ta fara yunkurin ɗaukar matakai rage kashe dala biliyan 2 da ake amfani da su wajen shigo da shinkafa daga ƙasashen waje, ta hanyar kafa Majalisar Ci gaban Shinkafa ta Ƙasa wacce za ta ƙarfafa noman shinkafa a gida da kuma bunƙasa samar da abinci.

Wannan kudiri ya fito ne daga Sanata Adamu Aliero, mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, wanda ke neman kafa hukumar da za ta daidaita bincike, ƙa’idoji, tallafa wa manoma, da kuma inganta kirkire-kirkire a harkar noman shinkafa a ƙasar.

Yayin sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio (ta bakin Mohammed Monguno wanda ya wakilta), ya ce matakan da kudirin ya ƙunsa suna cikin shirin sabunta tattalin arzikin ƙasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.

A cewarsa:

“Dokar Majalisar Ci gaban Shinkafa ta Najeriya za ta zama ginshiƙin ƙarfafa tattalin arziki, ta samar da ayyukan yi ga miliyoyin mutane, ta rage kashe kuɗin waje wajen shigo da shinkafa, tare da mayar da Najeriya cibiyar noman shinkafa a Afirka.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *