Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar

FB IMG 1772709275220

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin sauke  Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, daga mukaminsa bayan wani bincike da ta gudanar kan zarge-zargen da aka gabatar a kansa.

Majalisar ta kuma baiwa Mataimakin waadin mako biyu da yaje ya kare kansa.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta ɗauki matakin ne bayan nazari da tantance rahoton binciken da aka gabatar gabanta, wanda ya shafi zarge-zargen da suka haɗa da saba wa dokokin aiki da kuma wasu batutuwa da suka danganci yadda ake tafiyar da harkokin ofishinsa a bangaren kudi.

A cewar shugaban masu rinjaye na majalisar Hon. Husain Lawan Dala ,majalisar, ta ɗauki matakin ne biyo bayan bin dukkan matakan doka da tsarin aiki na majalisar, domin tabbatar da gaskiya da kuma kare martabar gudanar da mulki a jihar.

Majalisar ta kuma jaddada cewa an gudanar da binciken ne cikin tsari da adalci, tare da ba dukkan bangarorin da abin ya shafa damar bayyana matsayinsu kafin yanke hukuncin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa a hukumance daga ofishin Mataimakin Gwamnan ba dangane da matakin da majalisar ta dauka.

Ana sa ran cewa a cikin kwanaki masu zuwa za a samu karin bayanai daga bangarorin da abin ya shafa kan wannan lamari da ya dauki hankalin jama’a a Jihar Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *