Majalisar Najeriya Na Tuhumar Ministar Mata Kan Zargin Kashe N65m Ba Bisa Kai’da Ba

FB IMG 1715268720230

Majalisar wakilai ta tuhumi ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye da zargin kashe wasu makudan kudade ba gaura ba dalili, wadanda suka hada da Naira miliyan 45 na bikin sabuwar shekara da kuma Naira miliyan 20 wajen sayen audugar mata.

Sauran sun hada da Naira miliyan 1.5 na sayen man fetur da za a zuba a motoci.

Alfijir labarai ta ruwaito shugabar kwamitin harkokin mata ta majalisar wakilai Kafilat Ogbara ce ta jagoranci yiwa ministar tambayoyi kan rashin biyan ‘yan kwangila kuɗin su da ya kai naira biliyan 1.5 duk da an fitar da kuɗin a Abuja.

Ta ce an gudanar da zaman binciken ne domin gano gaskiya ba wai da manufar cin mutuncin Ministar da jami’an ma’aikatar ba.

Kwamitin ya kuma binciki zargin karkatar da kudaden da aka ware domin biyan ‘yan kwangila, biyo bayan koke daga ‘yan kwangilar.

Kwamitin ya kuma nemi karin haske kan kudaden da aka ware domin aikin matan shugabannin kasashen Afirka da kuma ba hadin inda naira biliyan 1.5 kuɗin ƴan kwangila.

Sai dai ministar ta musanta zargin karkatar da kudade, kashe kudade da kuma rashin biyan ‘yan kwangilan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *