Daga Aminu Bala Madobi
Kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na Majalisar Wakilai, ya ce ya karɓi buƙatar kirkiro jihohi 31 daga sasan ƙasar, domin ƙara yawan jihohin da ake da su guda 36.
Shugaban kwamitin Benjamin Kalu, wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar wakilai, ya bayyana hakan a zaman majalisar.
Ya ce, buƙatun sun haɗa da 6 daga Arewa ta Tsakiya, 4 daga Arewa ta Gabas, 5 daga Arewa ta Yamma, sai kuma 5 daga Kudu maso Gabas da 4 daga Yankin Kudu maso Kudu da 7 daga Kudu maso Yamma.
Ga jerin jihohin kamar yadda Kalu ya bayyana.
– Jihar Okun daga Kogi
– Jihar Okura daga Kogi
– Jihar Confluence daga Kogi
– Jihar Benue Ala daga Benue
– Jihar Apa daga Benue
– Jihar FCT daga FCT
– Jihar Amana daga Adamawa
– Jihar Katagum daga Bauchi
– Jihar Savannah daga Borno
– Jihar Muri daga Taraba.
– Jihar New Kaduna daga Kaduna
– Jihar Gujarat daga Kaduna
– Jihar Tiga da Ari daga Kano
– Jihar Kainji daga Kebbi
– Jihar Etiti da Orashi a yankin Kudu maso Gabas
– Jihar Adada daga Enugu
– Jihar Orlu da Aba daga Kudu maso Gabas
– Jihar Ogoja daga Cross River
– Jihar Warri daga Delta
– Jihar Ori da Obolo daga Rivers
– Jihar Torumbe daga Ondo;
– Jihar Ibadan daga Oyo
– Jihar Lagoon daga Lagos
– Jihar Ijebu daga Ogun
– Jihar Oke Ogun/Ijesha daga Oyo/Ogun/Osun.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ