Man United Ta Bayyana Tafka Wata Gagarumar Asara A Kakar Wasan 2021/22

Alfijr ta rawaito kungiyar Manchester United ta sanar da tafka asarar Yuro miliyan 115.5 a kakar wasan 2021/22.

Alfijr Labarai

Kungiyar ta sanar da hakan ne ranar Alhamis, in da ta ce kudaden shigarta sun karu zuwa Yuro miliyan 583 sakamakon sassauta dokokin kariyar COVID-19.

Red Devil ta ce a kakar wasannin wacce ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2022, bashin da ake bin ta ya karu zuwa kashi 22 cikin 100.

Sanarwar ta ce, darajar kungiyar wacce ta zama zakara a gasar Cin Kofin Ingila har sau 20, ta tashi daga Yuro miliyan 419 a 2021, zuwa Yuro miliyan 514 a bana.

Alfijr Labarai

Kungiyar ta alakanta karuwar bashin da faduwar da darajar Yuro ya yi a kan Dalar Amurka, lamarin da ya kara yawan kudaden.

Sauran abubuwan da suka jawo wa kungiyar tafka asarar sun hada da biyan ribar Yuro miliyan 33.6 ga masu hannun jari a cikinta da kuma biyan kudaden sallama ga tsohon Kocinta, Ole Gunnar Solskjaer wanda ta dakatar a watan Nuwamban 2021.

Amma kungiyar ta ce babban abin da ya jawo mata asarar shi ne karuwa kudaden da take biyan ’yan wasanta zuwa Yuro miliyan 384.2.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *