Kotu ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa kan laifin aikata fyaɗe a Jihar Kaduna.
Alfijir labarai ta ruwaito kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe.
Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata.
Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024.
An kama korarren jami’in tsaro da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai
EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba?
“Ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025 kuma Mai Shari’a B. Yusuf na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yanke wa na biyun hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya kan laifin fyaɗe.
“A ranar 24 ga watan kuma Mai Shari’a Isa Aliyu in yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai fa wanda wanda aka samu da laifin.”
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ