Martani: Sule Lamido ya Caccaki NSA Nuhu Ribaɗu kan kalamansa

IMG 20250214 114617

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Kuma tsohon Ministan Harkokin wajen Nageriya Sule Lamido lokacin da yake mayar da martani kan dambarwar dake tsakanin Nuhu Ribadu da Kuma kasar Canada yace, NSA da Shugabansa dole ne su fahimci cewa suna wakiltar ayyukanmu ne, darajar kasarmu ne a matsayin al’ummar kasa mai wayo!

Shekaru biyu da suka gabata sun tsumduma rikici da kungiyarmu ta dangantakarmu ta duniya da kuma ECOWAS, yanzu haka ga  Kasar Canada. Ya kamata duk wata Hauragiya ta tsaya tunda an bayar da izinin zama a duk lokacin da aka yarda ga ma’aikatar harkokin kasashen waje don basu damar taka rawar su a matsayin masu bibiyar  kare mu a matakin duniya.

Tsoma bakin NSA kan rikicin Hana Visa Ga Sojoji abu ne da Ya kamata ma’aikatar harkokin Waje ta maganceta ta Hanyar kwamishinan harkokin wajen Canada tare da tunkararsa da magana mai kyau domin cimma matsaya.

Amma NSA kawai ya tsoma baki a bayyane wanda hakan ka iya zubar da darajar da lalata alakar dake tsakanin Nageriya da Canada.

Ban so na saka baki ba kan wannan lamarin ba, amma soyayyar dake tsakanina da Nageriya ne yasa dole na saka baki.

Hakika  NSA bai daraja ma’aikatar Harkokin wajen Nageriya ba inji shi Sule lamido

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *