Masarautar Kano: An Sanya Tuta a Fadar Sarki Aminu Dake Nasarawa

FB IMG 1719482062345

Wayewar garin wannan rana ta alhamis an tashi da ganin tuta a saman gidan sarki na Nasarawa Inda mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune.

Alfijir labarai ta ruwaito wani bincike da muka gudanar tun ranar litinin a kafafen sada zumunta ake ta yada cewa za a saka tutar Shehu Usman Danfodio a gidan sarkin dake Nasarawa a birnin kano.

To Amma ba a saka tutar ba sai da safiyar wannan rana ta alhamis 27 ga watan yuni 2024.

Masana dai sun ce akan sanya tuta a duk gidajen Sarakunan da Shehu Usman Danfodio ya basu tutar Addinin Musulunci.

Ita kuma tutar tana nuna alama ce na cewa sarki yana gari ko baya gari.

Tuni dai wata majiya a gidan sarkin ta tabbatar wa da kadaura24 cewa tuni Sarki Aminu Ado Bayero ya nada sabon sarkin tuta, wanda aikin sa shi ne ya rika kula da tutar idan sarkin yana nan ko idan baya gari.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki kadan da gwamnatin jihar kano ta ware kusan Naira miliyan 100 domin gudanar da gyare-gyare a gidan sarkin dake Nasarawa, bayan tayi ikirarin rushe katangar gidan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *