Ministan Ilimin Nijeriya Malam Adamu Adamu Ya Bayyana Cewa Ya Gaza

Alfijr ta rawaito Ministan Ilimin Nigeria Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa ya gaza a matsayinsa na Minista.

Ministan ya yi wannan ikirari ne biyo bayan gazawarsa wajen warware kalubale da dama da ya kamata ya warware duk da kasancewarsa minista mafi dadewa a kan harkokin ilimi.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar ilimi na kasa karo na 66 a Abuja, ranar Alhamis.

Ministan ya kuma zargi ma’aikatun ilimi na jihohi da kara wasu abubuwan da suka taimaka masa wajen gazawarsa a matsayinsa na Minista.

Ya kuma bayyana cewa tun daga yaran da ba sa zuwa makaranta da ya karu a lokacin da yake kan mulki zuwa ga kalubalen kungiyar ASUU da sauran kalubalen da ke tabarbare harkar ilimin manyan makarantu, ya kasa samar da hanyar da ake bukata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *