Ministar Kudi Ta Gargadi CBN Akan Shirye-Shiryen Sake Fasalin Kudin Ƙasa

Alfijr ta rawaito Ministar Kudi, Kasafin Kudi Da Tsare-Tsare Ta Kasa, Zainab Ahmed, taki amincewa da Shirin babban Bankin Najeriya (CBN) na sake fasalin Naira, tana mai gargadin Babban Bankin, sakamakon matsalolin tattalin arzikin kasar.

Alfijr Labarai

Zainab ta bayyana rashin amincewarta da manufar ne a matsayin martani ga tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele ya yi a lokacin zaman kare kasafin 2023 da ta yi da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kudi.

Ministan ta gargadi CBN kan illar da ka iya tasowa daga atisayen.

Sanata Bamidele a cikin tambayarsa, ya shaida wa Ministan Kudi cewa kwanaki biyu bayan sanarwar da CBN ya fitar, ana jin tasirinta kan darajar Naira da Dalar Amurka.

Alfijr Labarai

Idan za a iya tunawa, Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele ya yi watsi da maganar a ranar Larabar da ta gabata, inda ya bayyana cewa atisayen da za a yi zai sake fasalin kudin Najeriya, daga N200 zuwa N1,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

3 Replies to “Ministar Kudi Ta Gargadi CBN Akan Shirye-Shiryen Sake Fasalin Kudin Ƙasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *