Al’umma a jihar Kano sun yi kukan kura sub kama gawurtaccen ɗan baban nan mai suna Abba Burakita a titin zuwa gidan gwamnati.
Alfijir Labarai ta rawaito bayanai dai sun bayyana cewa, an kama dan daban ne bayan da ya fito shi da yaransa su ka rika kwacewa mata wayoyinsu na hannu da babauran mutane da kudadensu .
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da ake wasan Polo a yammacin jiya Juma’a a Unguwar Nasarawa.
Majiyar ta ce mutane sun yi kukan kura ne inda su ka afkawa ‘yan dabar kuma nan take suka kama Abba Birakita, aka Kuma karya kafafuwansa da hannayensa .
Rahotanni sun tabbatar da cewa a halin yanzu haka ya na hannun yan sanda a Kano.
Birakita dai na daga cikin ‘yan dabar da suka mika kansu a kwanayin baya, bayan rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ayyana nemansa ruwa a jallo.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj