Allah ya yiwa Shahararren Mawakin tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida Alh Garba Gashuwa Rasuwa
Sanarwar ta fito ne daga bakin yar sa Maryam Garba Gashuwa kamar yadda ta shaidawa Jaridar Alfijir Labarai.
Maryam ta bayyana mahaifin nasu ya rasu ne a asibitin koyarwa na Murtala Muhammad Specialist dake Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da yaya da jikoki.
Daya daga cikin fitattun wakar da ta daga shi a lokacin rayuwarsa itace “Sannu da himma Uban kasa Babangida mai san gyara kasata”
Sai kuma wata wakar da ya dan takarar gwamnan jam’iyyar yiwa SDP a Kano, marigayi Engineer Magani Abdullahi, “Kai zakai Gwamna Baba in ma basu so ba”
Allah ya gafarta masa da sauran Al’ummar Annabi SAW.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya bibiyarmu a 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj