Daga Aminu Bala Madobi
Wata ‘yar Najeriya ‘yar asalin kasar Amurka, Victoria Ogunremi, ta mayar da makudan kudade da suka kai dala dubu 5,700 (kwatankwacin Naira miliyan 8.8 da ta samu a bandaki a wurin aikin ta da ke New Jersey, kasar Amurka.
An bayyana wannan karamci a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan gaskiya da kyautatawa wanda galibin ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ke yi.
Ogunremi da ta ke magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wata hira ta wayar tarho a ranar Litinin ta ce matakin ya samu yabo sosai daga ma’aikaciyar ta, abokan aikinta da kuma wanda ya yi asarar kudin.
A cewarta, ta yanke shawarar mayar da kudaden ne cikin damuwa ga wanda ya yi makuwa ya mance kudin.
“Ban yi jinkirin mayar da shi ba saboda bangaskiyar Kiristanci da imanina. Nuna halaccin gaskiya yana kawo kwanciyar hankali, kuma ita ce babbar ɗabi’a da nake ƙauna.”
Ta ce ta samu mai kudin kafin ta sanar da hukumar gudanarwar gurin datake aikin ta.
Ogunremi ta ce abokan aikinta su ma sun yaba da wannan karimcin nata, kuma da yawa ba su yi mamakin irin halin da ta yi ba.
“A irin tarbiyya ta, ta koya mana kada mu ɗauki abin da ba namu ba.
“Komai tsananin halin danake ciki, ko da yaushe ku rika mayar da abin da ba na ku ba. Yin hakan abin da ya dace ne kuma yana kawo lada mafi girma fiye da kowanne abu.”
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ