Daga Aminu Bala Madobi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da assasa dokar ta ɓaci akan tabbatar da tsaron Nigeria inda ya sanar da wasu sabbin tsare tsaren da su kara karfin tsaron da ake dashi a Nigeria.
Ga Jerin manufofi da Shugaban ya bada umarnin a sake dauka
1.. Shugaba Tinubu ya bukaci a kara yawan sojoji a duk yankuna da guraren da ake fama da matsalolin tsaro
2.. Shugaba Tinubu ya bayar da dama ga hukumomin soji da yan sanda akan su dauki karin jami’an tsaro, domin kara yawan jami’ai a bangaren tsaro.
3.. An sahale a dinga amfani da Sansanonin NYSC domin gudanar da horon sabbin yan sanda da zaa dauka a Nigeria.
4.. Shugaba Tinubu ya umarci babban safeton yan sanda akan duk yan sandan dake aikin bawa VIP tsaro dasu gaggauta komawa bariki sannan a tura su Training domin kara samun gogewa daga nan a turasu zuwa guraren da ake fama da matsalolin tsaro…
5.. An umarci hukumar DSS akan su tura horarrun jami’an FORREST GUARD wadanda aka horar zuwa cikin dazukan da Yan ta’adda masu garkuwa da halaka mutane suke, ta yadda zaa samu damar kawar da matsalolin tsaron dake tasowa daga dazuka…
6.. Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar DSS akan su dauki karin jami’ai tare da jami’an Forrest Guard..
7.. Gwamnatin za ta tallafa wa gwamnatocin jihohi da suka kafa ƙungiyoyin tsaro…
8.. An shawarci jihohi su sake tunani game da kafa makarantun kwana a yankunan da ba su da isasshen tsaro…
9..An yi kira ga masallatai da coci-coci su nemi kariyar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro akai-akai lokacin da suke taruwa don yin ibada a wuraren da ke cikin haɗari….
10.. Warware Matsalar Makiyaya da Manoma: Ya kira dukkan ƙungiyoyin makiyaya su yi amfani da sabuwar Ma’aikatar Livestock domin anfanuwa da tsare tsaren da akayi saboda su, sannan an bukaci duk wasu masu yawan kiwo dauke da makamai akan su mika makamansu nan take don kaucewa haduwa da fushin hukuma…
Wadannan suna daga cikin jawaban da shugaba Tinubu yayi a wannan rana domin daukar matakin gaggawa mai inganci wanda zai dore akan matsalolin tsaron Nigeria, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa tsaron kasa shine aiki mafi girma da ya sanya gaba kuma ba zai taba gajiyawa ba sai ya tabbatar al’umma suna zaune cikin kwanciyar hankali da izinin Allah
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t