Remi Tinubu ta mikawa Gwamnan Kano tallafin miliyan 110 ga iyalan yan wasan da suka mutu a hadarin mota

IMG 191544 28625 1751134562106

Uwar gidan Shugaban kasa Bola Tinubu Mrs Remi Bola Tinubu ta mika ta’aziyarta ga iyalai da yan uwan yan wasan kwallon kafa 22 da suka mutu a hadarin mota.

Remi wacce ta bayyana rashin yan wasan a matsayin babban rashi tayi fatan Allah ya ji kansu kuma ya baiwa iyalansu hakurin rashin.

Uwar gidan Tinubu wacce ta samu wakilcin uwar gidan mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibiril wato Hajiya Laila Barau Jibiril, ta ce kowanne iyali na mamatan zai samu naira miliyan biyar.

Wakiliyar ta uwar gidan Shugaban kasa da tawagarta ta mika cekin kuɗin ne ga gwamna Abba Kabir Yusuf a ofishinsa a lokacin ziyarar da suka kawo masa a yammacin Asabar.

Ta kuma mika sakon ta’aziyarta ga rashin da akayi a Kano dama kasa baki daya na dattijo Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Da yake nasa jawabin,gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya godewa uwar gidan Shugaban kasa tare da shaida cewa ba wannan ne karo na farko da take nuna jin kanta ga mutanan Kano ba.

Gwamna Yusuf yace ko a Kwanakin baya sai da ta tallafawa matan kano da kuɗi naira dubu biyar Inda mata sama da dubu biyar suka amfana.

Gwamna Abba yace domin yin komai a bude cikin gaskiya, shiyasa ya gayyaci iyalan matasan da suka mutu domin su shaida abin da aka basu kuma su yiwa matar Shugaban kasa godiya.

Haka zalika gwamna Yusuf ya godewa dukannin wadanda suka tallafawa iyalan mamatan musamman gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun da ya bada tallafin naira miliyan 32 da gwamnan jihar Jigawa da ya bada tallafin naira miliyan 22 da sauransu.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *