A ranar Alhamis ne zauren majalisar dattawan Najeriya ya dauki zafi lokacin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta fito fili ta nuna rashin jin dadinta game da canjin kujerar da akayi mata ba tare da sanarwa ba. Wannan lamari ya kai ga rikici tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Sanata Natasha ta bayyana rashin gamsuwarta da cewa: “Bana jin tsoronku.” Wannan furuci ya fito ne yayin da ta ke kokarin kare kanta daga matakin da ta bayyana a matsayin tauye mata hakki. Shugaban majalisar, a martaninsa, ya nemi ta zauna ko kuma ta bar zauren, amma Natasha ta dage tana mai cewa dole a fahimtar da ita dalilin wannan canji.
Tashin hankali ya janyo hankalin sauran sanatoci, wadanda suka shiga tsakani domin daidaita lamarin. Wasu sun bayyana cewa sauye-sauyen kujerar na iya zama abin da ya faru sakamakon wasu gyare-gyare dake gudana a majalisar.
Daga karshe, majalisar ta cigaba da zamanta bayan shugabanni sunyi kira ga sanatoci subi dokoki da ka’idoji wajen warware duk wata matsala, ba tare da haifar da hayaniya ba
Sanata Natashi cikin fushi ta zargi shugaban majalisar da yi wa yankin Arewacin Nijeriya zagon Æ™asa, ta ce “Duk abinda zai kawo Æ™aruwa a Arewacin Æ™asar nan, wannan shugaban majalisa sai ya yi iya yinsa ya rusa abin saboda ba yankinsa ba ne.” Inji ta.
Shugaban majalisar ya hana Sanatar magana saboda ta taso da maganar aikin yashe kogin kwara da zuwa yanzu aka daina aikin, inda tayi zargin an yi hakan ne saboda kada Arewacin Nijeriya ta samu ci gaba, kuma haka ne ya sa, ya rusa maganar da ta kawo.
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ