Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Wani Shiri Na Kawar Da Amfani Da kananzir A Kasar.

Alfijr ta rawaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani sabon tsari a cikin wani sabon salo na kawar da amfani da kananzir a kasar, nan da shekarar 2030.

Buhari ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya shirya kan kungiyar Tattalin Arziki kan Makamashi da Sauyin yanayi (MEF), ta ce wani bangare ne na kudirin Najeriya na samar da yanayi mai inganci da lafiya.

Alfijr

A tattaunawar da yayi da gidan talabijin na Channel, Shugaban kasar ya kuma lissafta tsarin bayar da gudummawar da aka sabunta na kasar nan, wanda ya hada da karuwar amfani da motocin bas a cikin a matsayin ababan sufuri ga jama’a, kashi 50 cikin 100

Ya bayyana cewa, NDC gudunmawa ce ga yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da sauyin yanayi, wanda aka gabatar don maye gurbin gudunmawar wucin gadi na Mayu 27, 2021.

Alfijr

A cikin 2012, gwamnatin tarayya ta fara sabon daftarin manufofin da aka sani da National Strategic Policy for LPG tare da haɗin gwiwar. tare da masu ruwa da tsaki a masana’antar man fetur, don kawar da kananzir da amfani da shi a cikin ƙasa tare da ɗaukar iskar gas ɗin dafa abinci a matsayin madadin.

Slide Up
x