Rundunar Yan Sandan Kano ta bayyana dalilin Karrama Wakilin Muhasa TV & Radio

IMG 20250314 WA0001

Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta karrama daya daga cikin ma’aikatan tashar MUHASA Telabijin da Radio, Mujahid Wada Guringawa, saboda kwazo da jajircewa da ya ke yi wurin gudanar da ayyukansa tare da bayar da rahotonin rundunar wajen wayar da kan al’umma kan abinda ya shafi tsaro da zaman lafiya a jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan, a wajen bikin karrama kwamishinan yan sandan jihar, mai barin gado, AIG Salman Dogo Garba, da ya samu karin girma zuwa mataikamakin babban sufeton yan sandan Nijeriya.

Mujahid Wada, ya yi fice a tsakanin abokan aikinsa wurin zakulo labaran da suka shafi rundunar yan sandan don tabbatar wanzuwar zaman lafiya a jihar Kano baki daya.

Bikin karramawar da ya gudana a wajen shakatawar manyan jami’an yan sanda dake Bompai Kano.

Rundunar ta godewa tashar Muhasa, tare da yi musu fatan alkairi wajen ci gaba da gudanar da aiyukansu na wayar kan al’umma a bangarorin rayuwa daban-daban.

Kwamishinan yan sandan Jihar Kano mai barin gado, AIG Salman Dogo Garba, ne ya mikawa Mujahid wannan lambar yabo a helkwatar rundnar yan sandan dake unguwar Bompai.

Haka zalika , AIG Salman Dogo, bayan Karin girman da ya samu ya samu sauyin wajen aiki, inda zai kula rundunar yan kasa ta kasa a shiya 5 wadanda suka hada da jahohin Edo da kuma Delta.

Da yake bayyana farin cikinsa wakilin tashar Muhasa TV da Radio,Mujahid Wada Guringawa ,  ya ce wannan wata Allura ce wadda zata kara zaburar dashi, don yin abinda zai habbaka tashar da yake gudanar da aikinsa.

Ya kuma yi kira al’umma da a duk lokacin da suka ga wani abun zargi da su baa mince da shi ba, su gaggauta sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace.

Shugaban kwamitin aikin tsaro da al’umma PCRC na jihar Kano, Dokta Ali Hassan Tudun Bayero ya godewa,  AIG Salman Dogo,  bisa aikin da ya yi wajen dauwamar da zaman lafiya a Kano.

Yan uwa abokan aiki na tashar MUHASA TV & RADIO tuni suka taya Mujahid Wada murna tare da yi masa fatan alkairi da ci gaba da jajircewa a koda yaushe.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *