Daya daga cikin matasan jam’iyyar APC na karamar hukumar Dala, kuma hadimi ga kakakin majalisar wakilai, Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, ya raba tallafin miliyoyin kudi ga shugabannin jam’iyyar karamar hukumar, da sauran magoya baya don su samu farin ciki da walwala a wannan lokaci na Azumin Ramadan.
An kaddamar da rabon tallafin a yau Alhamis wanda dumbin magoya bayan APC daga karamar hukumar ta Dala, da sauran kananun hukumomi suka halarta don nuna goyon baya da yabawa ga Hon. Abubakar Aminu Ibrahim.
Daga cikin mutane dubu 1 da suka amfana da tallafin an bawa wasu Naira dubu 50 kowanne mutum daya, sai masu dubu 20 kowanne mutum daya da kuma masu dubu 10-10.
Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, yace wannan ba shine karon farko da ya fara bayar da tallafi ga al’ummar karamar hukumar Dala ba, sakamakon cewa a baya ya bayar da tallafin fom din rubuta jarrabawar samun gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire wato JAMB ga matasa 250.
Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, ya kara da cewa wadannan abubuwan alkairi da yake yi ya kwaikwayo su ne daga wajen dan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi wato Abba Bichi, da kuma Ganduje.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, shine ya kaddamar da rabon kudin wanda kakakin jam’iyyar Ahmad Aruwa ya wakilta.
Aruwa, yace gwmanatin Kano mai ci tayi abun kunya saboda a cewar sa NNPP ta gaza bayar da tallafi ga al’ummar jihar Kano duk da cewa tana rike da mulki, amma APC tana aiwatar da ayyukan tallafawa mutane tun daga mazaba zuwa matakin jiha.
Yace Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, yayi kokari wajen bayar da wannan tallafi wanda irin hakan zai kai shi ga matsayin da ba’a taba zato ba, a siyasar Kano da kasa baki daya.
Ya kuma roki magoya bayan APC dasu fito su tallafawa al’umma a wannna hali, musamman abinci, aikin yi da sauran su, yana mai cewa ba sai da Azumi kadai ya kamata a taimakawa mutane ba. Sannan ya yabawa daukacin yan APC da suke bayar da taimako ga al’umma.
Itama shugabar matan APC ta jihar Kano Hajiya Fatima Abdullahi Dala, tace wannan tallafin da aka bayar tun daga mazaba zai sanya farin ciki a zukatan yan jam’iyyar APC, daga kan masu rike da shugabanci zuwa kan sauran yan jam’iyyar. Sannan ta yaba akan yanda aka fifita mata wajen bayar da tallafin.
Bayan haka tace wannan aiki da Abubakar Aminu, yayi aiki ne irin na mai dakin shugaban APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wato Hafsat Ganduje.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Alin Ummi, Ibrahim Hamza Ibrahim da kuma Hadiza Sulaiman, sun bayyana jin dadin su akan aikin alkairi tare da alwashin tallafawa Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, a duk lokacin da yake neman taimakon yan jam’iyyar, ko ya tsaya wata takara.
Manyan shugabannin APC na jihar Kano sun samu damar halartar taron, wanda suka hadar da Musa Iliyasu Kwankwaso, Ahmad Aruwa Liti Kulkul, Nasiru Aliko Koki, Manniru Haruna, da sauran su.




Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD