Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Ambassada Abdu Zango ya ce akwai sama da katin zabe 360,000 da har yanzu masu su basu zo sun karɓa ba a jihar Kano
Yayi wannan bayanin ne yayin da kwamitin wayar da kan al’uma kan muhimmancin mallakar katin zabe, karkashin jagorancin Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya suka kai masa ziyara a yau asabar a ofishin su dake Kano.
Zango ya bukaci kwamitin da ya wayar da kan waɗanda suka yi rijista su zo ofishin hukumar domin karbar katinsu.
Shugaban ya yabawa gwamnatin Kano na wannan yunkuri domin taya su wannan gangamin wayar da kan ga al’umma, ya kuma yabawa kwamitin da fatan samun nasara akan aikin da ciyar da jihar Kano gaba
Da yake mayar da martani shugaban kwamitin kuma Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Camarde Ibrahim Abdullahi Waiya yace, gwamnatin jihar Kano ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta samar da karin rumfuman zabe a mazabun jihar Kano 484 domin rage cunkoson da ake fuskanta a lokacin zabe.
Kwamared Waiya ya ce an samu karin sabbin gundumomi da unguwanni a jihar Kano, wadanda suke bukar a shigar dasu cikin jadawalin hukumar, inda ya kuma bukaci a rage alkaluman rumfuman da ake samun cunkoso zuwa sabbin rumfuman zaben da za a kirkira.
Ya kara da cewar a shirye kwamitin yake ya yi kafada-da-kafada da hukumar domin wayar da kan al’umma tare da taimaka musu ta kowace fuska.






Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t