Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Jihar Kano

Police

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, sashin kwantar da tarzoma za su gudanar da atisayen harbin Bindiga daga ranar Alhamis 5 ga watan Satumba zuwa juma’a 6 ga watan Satumba 2024.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari a daren Talata nan.

Ya ce Yan Sandan kwantar da tarzoma Mai 52 dake Challawa , sune za su gudanar atisayen harbin Bindigar, a kebantaccen wurin nan hawan Kalebawa, dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa za a fara atisayen harbin tun daga karfe 6:00am zuwa 6:00pm na yammacin ranakun.

kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya shawarci mazauna yankin musaman , Danbazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalan dake kananan hukumomin, Dawakin Tofa da kuma Ungoggo, da su kauracewa wajen kuma kar su firgita dajin karar harbin da za suji har sai an kammala.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *