A jiya ne kungiyar gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP-GF) ta gargadi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya daina furta kalamai masu tayar da hankali da ka iya hargitsa jam’iyyar.
Alfijir Labarai ta rawaito Darakta Janar na kungiyar, Dokta Emmanuel Agbo, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, barazanar da Wike ya yi wa kungiyar ta zama barazana ga hadin kai da zaman lafiya a jam’iyyar.
Wike, jigo a jam’iyyar PDP, ya caccaki gwamnonin kan yadda suka yi tsoma baki a rikicin siyasar Ribas da ya dade yana mai cewa zai haifar musu da rikici a jihohinsu.
Sai dai, ban da wadannan kalamai, kungiyar ta ce barazanar da Wike ke yi na “harba wuta” a jihohin da PDP ke mulki, “Rashin hankali ne, Kuma ba za a amince da shi ba.”
A cewar kungiyar, tsohon gwamnan yana yin zagon kasa ga kokarin ginawa da wanzar da zaman lafiya da hadin kai da mutunta juna a tsakanin shugabannin jam’iyyar da mambobin jam’iyyar.
Sun kara da cewa: “Kungiyar tana kira ga shugabannin hukumomin tsaro na kasa da su lura da barazanar da Wike ke yi na tada wutar rikici a jihohin da PDP ki mulki domin babu wanda ya fi karfin dokar kasa.
“Abin takaici ne cewa wannan yana fitowa ne daga wani wanda ya taba zama memba a wannan dandalin da ake girmamawa a matsayin tsohon gwamna.”
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj