Shugaba Tinubu Ya Bawa Dangote Da BUA Umarni Akan Siminti

FB IMG 1706824949754

Shugaba Tinubu ya umurci kamfanonin siminti da su dawo sayar da simintin akan tsohon farashi kamar yadda yake a baya a Nigeria.

Alfijir labarai ta rawaito ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ya ziyarci masana’antar siminti ta BUA da ke Sokoto ranar Alhamis.

Ministan ya ce a ganawar da ya yi da masana’antun, shugaban ya umarce su da su dawo sayar da simintin a kan farashin baya.

“Ina so in ba su kwarin guiwa da su bi umarnin shugaban kasa domin mu cimma gagarumin shirin samar da gidaje da kuma sabon tsarin sabunta fata da shugaban kasa zai yi,” in ji shi.

“Lokacin da shugaban kamfanin ya ziyarci shugaban kasa a makon da ya gabata, saboda kokarin sa na inganta aiyukan sa” in ji shi.

Sai dai ya yabawa mahukuntan kamfanin bisa tabbatar da tsafta a daukacin harabar kamfanin.

Ministan wanda ya samu rakiyar shugaban kwamitin majalisar dattijai akan harkokin gidaje, Sanata Aminu Tambuwal, ya ce gwamnatin tarayya ta fara aikin titin kilomita 372, mai hannu biyu daga Zaria zuwa jihar Sokoto.

“Na zo nan ne domin in ga al’amura da kaina, kamar yadda kuka sani, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta fara aikin titin mai tsawon kilomita 372 wanda kashi na farko za a yi shi ne da kwalta, yayin da sauran za a yi da kankare.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a yan Kwanakin nan sai da ya zamo ana sayar da buhun siminti har Naira Dubu goma har zuwa 15 a wasu jihohin kamar Abuja.

Kafin wannan lokaci dai ana sayar da buhun simintin akan kuɗi Naira Dubu hudu zuwa biyar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *