Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban gidan talbijin na Ƙasa NTA, Salihu Abdullahi Dembos, wanda aka sauke kwanakin baya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata da maraice ya ce Dembos – wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023 – zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku.
A kwanakin baya ne aka sauke Dembos daga kan muƙaminsa duk da cewa wa’adinsa bai cika ba, lamarin da ya jawo suka daga wurin mutane da dama.
Kazalika Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin mayar da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA domin shi ma ya kammala wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t