Shugaba Tinubu ya zaɓi sabon shugaban hukumar Alhazai ta Najeriya Amb. Ismail Abba Yusuf

FB IMG 1770829573772

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya zaɓi Amb. Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON).

Wata sanarwa da ta fito daga mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga, ta ce a yau Laraba ne shugaba Tinubu ya aike da wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci a gaggauta tabbatar da Ambasada Yusuf ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a farkon wannan makon, bayan shafe kimanin watanni 14 yana kan muƙamin.

Ambasada Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyya ne wanda ya taɓa zama jakadan Najeriya na musamman kuma mai cikakken iko a ƙasar Turkiyya daga 2021 zuwa 2024.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *