Hukumar Shari’a ta jihar Kano Karkashin Jagorancin Shugabanta Malam Abbas Abubakar Daneji, ta jagoranci zama na farko wanda ya gudana domin ganawa da sauran Shuwagabannin hukumar da suka hada da;
Permanent Commissioner I : Malam Hadi
Permanent Commissioner II : Sheikh Mal. Ali Danabba.
Sai kuma sauran mambobin hukumar duk sun hallara a wannan rana ta laraba, 19 ga Watan Fabrairu, 2024,
Taron ya mai da hankali ne wajen irin kalubalen da ke gabansu na yadda aka dora musu nauyin akan abinda ya shafi shari’a a fadin jihar Kano, duba da yadda al’umma musamman yan kasuwa suke cin karen su babu babbaka, sai kuma yadda aka zuba ido a jihar Kano wasu bata gari ke amfani da social media wajen cin mutuncin al’umma da batanci ga addini.
Don haka an cimma matsaya aka kwamatin zai dinga ziyarar al’umma daban da kasuwanni da masana’antu a jihar domin tunatar da su hanyar Allah ko a samu a rabauta duniya da lahira









Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ