Daga mustapha salisu_
Shugaban kamfanin Sagama LTD Alhaji Ali Nuhu, ya dauki nauyi sakin fursunoni 12, a gidan gyaran hali da tarbiyya na kurmawa, a wani ɓangare na jin kan al’umma da ya saba yi.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala dakin wadanda aka wa afuwar masu kanana laifuka Alhaji Nuhu Rabiu ya ce, ya sami kwarin guiwar yin wannan aikin ne karkashin Shawarwarin da shugaban Kamfanin Tubless Media Concept, Nasiru Rabiu Tubless yake bashi a kowa ne lokacin domin kin kan al’umma.
“Wannan shi ne karo na farko da ke ziyartar cibiyar gyaran hali da tarbiyya, kuma da abin da na gani ya taba min rai,” in ji shi. “
Nuhu ya bukaci wadanda suka sami shaƙar iskar yanci da za su yarda da ƙaddarar da ta fada musu na zaman gidan a matsayin jarraba, kuma hakan zai musu darasin rayuwa, kuma ya ja hankalin su wajen aikata manya da kananan Laifuka su zaman to jakadun kwarai.
Da yake karin haske kan wannan aikin Ibrahim Ahmadu, tsohon shugaban reshe na Stanbic, ya bayyana cewa Alhaji Nuhu ya ware kimanin N500,000 don tabbatar da sakin fursunoni, wanda ya haifar da fitar da mutane 12, kuma yace wannan shine karo na farko kuma zasu cigaba da nemo wadanda suka hadu da ibtila’in rayuwa domin yi musu afuwar.
Hakazalika Ahmadu ya shawarci wadanda aka yiwa afuwar da su nemi gafarar Allah, da ci gaba da girmama iyayensu, da kuma tsayawa wajen dogara da kansu.
Ya kuma yabawa shugaban kamfanin Tubeless bisa yadda yake ci gaba da tallafa wa jama’a ta hanyar koyar da sana’o’in hannu da kuma amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen wayar da kan jama’a da dogaro da Kai.
“A kan haka ne muka yi tattaki daga Abuja zuwa Kano domin yaba wa kokarinsa, mun kuma ziyarci gidan marayu inda muka raba kayan abinci tare da karfafa wa yaran gwiwa su ji su ma kamar kowa suke. Ina Ji shi.
A nasa bangaren, Shugaban Kamfanin Tubless Media Concept, Nasiru Rabi’u Tubeless, ya bayyana kadan daga tarihin Gwagwarwa da suka sha a baya
“Mun yi duk wannan ne saboda Allah. An taba tallafa mana a rayuwa, kuma yanzu lokaci ya yi da za mu rama wa kura aniyar ta,” in ji Tubless.
Shugaban Kamfanin Sagama daganan ya kuma bayar da kudin mota ga fursunonin, sannan ya yi alkawarin tallafawa bukatunsu na yau da kullum da suka hada da samar da masana’antar dinki.
Tubless ya tabbatar da cewa ire iren wadannan faifan bidiyon nasa zai ci gaba da jan hankalin masu hannu da shuni don tallafawa cibiyar ta hanyoyi daban-daban. Ya kuma shawarci al’umma gaba daya da su nisanci munanan dabi’un zamantakewa kamar shaye-shayen miyagun kwayoyi da satar mutane, wadanda galibi ke kai mutane gidajen gyaran hali.
Wani dan uwan daya daga cikin fursunonin da aka sako Usman Sani Gwangwazo ya bayyana yadda suka samu labarin cewa an sako dan uwansa.
Muhimman abubuwan da suka faru a taron sun hada da rangadin dakunan koyon sana’o’i da na likitanci, kamar aikin tela, dakin gwaje-gwaje, da kuma asibiti.
Alhaji Nuhu ya kuma yi alkawarin gabatar da wani tagomashi ga fursunonin, inda ya fara da tallafin kudi naira 50,000 don koyon sana’o’i ga sassan biyu na Gidan Gyaran Halin Da kuma samar da na’urar busar da gashi a bangaren mata.




Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t