Shugaban Najeriya ya ƙara naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kuɗin 2024

FB IMG 1719960146800

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bukaci majalisar dattawa da ta yi wa dokar kasafi ta 2024 da kuma dokar kudi ta 2023 gyaran fuska ta hanyar amincewa da ƙarin naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin kuɗin.

Alfijir labarai ta ruwaito buƙatar ta Tinubu na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Laraba.

A cikin wasikar, Shugaban ya ce yana son ɗaukar matakin ne bisa dogaro da sashe na 58, ƙaramin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska.

Wasiƙar ta ce “Ana buƙatar yin gyara ga ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2024 don samar da ƙarin naira tiriliyan 3.2 don ayyukan more rayuwa da sauran muhimman ayyuka da za a gudanar a faɗin ƙasar.

“Da kuma naira tiriliyan uku don biyan wasu buƙatu na yau da kullum, waɗanda suka dace don gudanar da ayyukan na tafiyar da harkokin gwamnatin tarayya, waɗanda za a samu ta hanyar kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayyar Najeriya ke sa ran samu,”

Tinubu ya ƙara da cewa ana buƙatar aiwatar da gyare-gyaren da ake neman yi wa dokar kuɗi ta 2023, domin a sanya haraji kan ribar da bankuna suka samu a cikin bayanan kudi na shekarar 2023.

Ya yi bayanin cewa an yi hakan ne don samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wurin bunƙasa manyan ababen more rayuwa a fannin ilimi da kiwon lafiya, da sauran ayyukan jin dadin jama’a.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *