Soja Ya Bindige Kwamanda Da Wasu Sojoji 2 A Nijeriya

Alfijr ta rawaito wani fusataccen sojan Nijeriya ya dauki bindiga ya kashe Kwamandansa, da wasu sojoji biyu, daga bisani ya kashe kansa da a sansanin ‘Forward Operating Base’, Rabah da ke jihar Sokoto.

Sojan mai suna Lance Corporal Nwobobo Chinoso yana aiki a karkashin bataliya ta 223 da ke Zuru ta jihar Kebbi, an kuma tura shi aiki sansanin Forward Operating Base Rabah, in da lamarin ya faru ne a gidan Kwamandan sansanin a ranar Lahadi.Nwobobo bude wuta ne nan take ya kashe Kwamandan FOB, Lt. T.I. Sam-Oladapo, da wasu sojoji biyu ciki har da Sajen Manjo (CSM), Iliyasu Inusa da Private Attahiru Mohammed, daga bisani ya juya bindigar zuwa kansa.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Maris na 2023 da misalin karfe 5 na yamma, sannan har zuwa yanzu ba a iya gano musabbabin bude wutar ba, amma ana  kaddamar da bincike kan lamarin.Kwamandan runduna ta 8 Garrison da Kwamandan bataliya 26 sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Hakazalika an kwashe gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio (UDUTH) da ke Sokoto.

A kokarin jin ta bakin daraktan sashin yaɗa labarai na rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar, Onyema Nwachukwu, amma lamarin ci tura, sai sai wasu majiyoyin soja sun tabbatar wa leadership da faruwar lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *