Ranar Mata ta Duniya Da Ranar Masu Amfani da Keken masu bukata ta musamman na Duniya na iya zama banbarakwai da ba a saba da su ba la’akari da rashin alaƙar su da jama’a, amma suna tarayya da juna – wajan inganta daidaito, haɗa kai, da ƙarfafawa.
Ranar keken masu bukata ta musamman ta duniya, wadda aka gabatar da bikin a ranar 1 ga Maris, Makasudin ta haɓaka kyakkyawar fahimta game da masu amfani da keken masu bukata ta musamman, tsame duk wani shinge da magance matsaloli masu amfani da shi, da bayar da shawarwari don samun daidaito ga kowa.
Rana ce da ake gabatar da ita don nunawa mata da masu amfani da keken guragu irin muhimmancin su cikin al’umma don haɓaka basu damammaki a dama dasu da bayar da shawarwari don fidda haƙƙin masu amfani da keken guragu a duniya.
A daya bangaren kuma, ana gabatar da ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris, rana ce ta nuna irin nasarorin da mata suka samu, da wayar da kan al’umma kan ‘yancin mata, da inganta daidaiton jinsi.
Idan mukayi amfani da damar wajan haɗe waɗannan bukukuwa guda biyu, za mu ƙarfafa muryar mata masu bukata ta musamman tayi nisa ta karade ko ina don girmama matan da ke yawo a duniya a keken guragu, suna nuna bajinta da ƙarfinsu, azama, da karfin gwiwar su na rashin nuna gajiyawa kan kowanne irin ƙalubale dasuke fuskanta.
Matan da ke hawa keken masu bukata ta musamman suna kunshe da haɗakar alherai da juriya mai ban sha’awa. Nazarin yadda suke rayuwa na musamman ne da na gama gari.
Ta yiwu suna iya shawo kan dukkan irin kalubalen dake taso musu cikin al’umma, su iya magance shi, mata masu bukata ta musamman na ci gaba da rayuwa kamar kowa tareda tabbatar da bayyana ƙwarewar su a fannonin rayuwa, kuma muryoyinsu masu ƙarfi ne da za a iya jiyosu a ko ina.
Ranar mata ta duniya da na masu hawa keken masu bukata ta musamman ta duniya ta zamo wata manuniya dake haska cewa kowacce mace ta cancanci samun damar ci gaba kamar kowa, ba tare da la’akari da yanayin da suke ciki ba.
Rana ce don girmama irin nasarorin da suka samu, da ba da labarinsu, da kuma ɗaga likafar al’ummomin su daban-daban adama dasu cikin ayyukan gwamnati.
Yayin da muke cigaba da murnar zagayowar wannan rana, ba wai kawai iya nasarorin da suka samu ba ne abin bayyana wa, har ma da sadaukarwa da nemawa kansu mafita don tabbatar da samun ingantacciyar rayuwa kamar kowa.
Hakika kowacce mace, ba tare da la’akari da irin rayuwar da ta keto ba, wata alama ce jajircewa. Tare da juna, muna murna da irin sadaukarwa, juriya, kyawun zamantakewa, da ƙarfin hali don cimma nasara.
Don haka, bari mu yi amfani da wannan dama wajen nuna farin ciki da azama na mata masu bukata ta musamman, tare da yin aiki tare don ganin an samu makoma ta yadda kowa zai samu dama daidai gwargwado don samar da al’umma mai tausayi, hadin kai dakuma adalci a zamantakewar mu.
“Atare Zamu yi Nasara. Ƙarfafa Muryoyin Mata Masu Rauni Da Masu Bukata Ta Musamman”.
Na gode.
Engr Abdul Haruna, moi, coh.
Mai Fafutika Ga Masu Bukata Ta Musamman.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ