TIGMEIN Zata Bawa Mutane 500 Tallafi A Jihar Kano

Daga
Bilkisu Yusuf Ali

Alfijr ta rawaito kungiyar Tijjaniya Grassroots Mobilization And Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMAIN) reshen jihar Kano ta shirya tallafawa mambobinta.

Bayanan haka na kunshe ne cikin wani taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki na kungiyar ranar 6/11/2022 a Unguwar Kurna da ke jihar Kano.

Taron an tattauna hanyoyin da za a bi don tabbatuwar wannan kudirin na bayar da tallafi maza da mata, kuma tallafin mai tsoka ga mutum dari biyar na jihar Kano wadanda suka fito daga kananan hukumomi arba’in da hudu.

Shugaban riko na Kano Injiniya malam Rabiu Pansheka ne ya tabbatar da haka a yayin zaman.

Daga cikin shirye-shiryen da ake son a gabatar a ranar akwai kaddamar da shuwagabannin kungiyar na jihar.

Sai kuma gudanar da wannan tallafi ne ga al’ummar jihar Kano don sanya al’umma su dogara da kansu da kansu.

A tsarin wannan tallafin za a koyar da sana’oi na bangaren mata da maza, sannan a tallafawa wadanda suka koyi wannan sana’ar da jarin ci gaba da gudanar da sana’ar.

Ya kuma kara da cewa irin wannan lokacin ya zama wajibin al’umma duk wanda yake da hali ko yake da ilimin wata sana’a ko hanyar koyon wata sana’a da ya bayar da hadin kai don al’umma ta karu, saboda fita daga wannan matsatsi da al’umma ke fuskanta a yau.

Shugaban kungiyar na riko kwaryar na jihar Kano, ya kuma yaba wa ‘yan kungiyar na jihar Kano bisa aikin da suke yi ba dare ba rana don tattaro ‘yan dariqar Tijjaniya da zawiyoyi sako da lungu birni da kauye na jihar Kano da fito da su don a samu haxin kai da taimakekeniya tsakanin juna da zama inuwa guda.

Ya ƙara da cewa hakika iya wannan kadai babbar nasara ce a tafiyar TIGMEIN.

Kungiyar TIGMEIN kungiya ce ta kasa kuma ta hadin kan mabiya dariqar Tijjaniya na kowanne bangare na kowacce zawiyya ba tare da kowanne irin bangaranci ba.

Hakazalika tuni ire-iren wannan tallafin da hadin kan ya yi nisa a wasu jihohin a kasar nan, kamar yadda shugaban wannan kungiyar na kasa Shehu Tijjani Sani Auwalu wanda jika ne ga Shehi Ibrahim Niasss.

Taron ya samu halarta coordinators na Kano ta Arewa da Kano ta tsaliya da kano ta kudu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

2 Replies to “TIGMEIN Zata Bawa Mutane 500 Tallafi A Jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *