Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Kano zuwa Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule.
Marigayi Alhaji Maitama Sule, wanda ya rayu tsakanin shekarar 1929 zuwa 2017, ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar Nijeriya a tsawon rayuwarsa.
Marigayin ya taba zama wakilin Najeriya na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, inda ya kasance shugaban kwamiti na musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da wariyar launin fata.
Ya kuma kasance dan majalisa kuma mai tsawatar a majalisar wakilan Najeriya tsakanin 1954 zuwa 1959.
Sannan shine kwamishina na farko a hukumar karbar korafe korafe ta Kasa a shekarar 1976,kafin daga bisani ya zama ministan ma’aikatar ma’adanai ta kasa.
A Kano kuma ya rike mukamai da dama ciki harda kwamishinan yada Labarai.
A wata takarda da mai magana da yawun Shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar yace Shugaban Tinubu yayi amanar cewa sanya sunan Marigayin Maitama Sule a jami’ar ta gwamnatin tarayya dake Kano zaisa a cigaba da tunawa dashi.
Haka kuma yace hakan zai zaburar da matasa masu tasowa su yi koyi da halayensa musamman tabbatar da gaskiya da kishin kasa da halaye na gari da aka san Dan masanin Kano dasu tun yana raye
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ