Tinubu Ya Bada Buhunan Shinkafa 1,200 Ga Kowane Minista Don Tallafawa Al’umma

FB IMG 1723115651747

Ministan ma’adanai Dr. Dokta Alake ya bayyana cewa, “A matsayin martani ga matakin da fadar shugaban kasa ta ɗauka na magance Bukatun ‘yan Najeriya ta hanyar ƙara samar da abinci a matakin kasa, An ware buhunan shinkafa 1,200 ga kowane minista Domin ƙara samar da hanyoyin rarraba kayayyakin da ake da su kamar Gwamnatocin jihohi da kungiyoyin jama’a. ”

Alfijir Labarai ta rawaito ministan ya kara da cewa, “Za mu tabbatar da cewa wadannan tanade-tanaden an yi su ne ga tsofaffi kawai. A irin waɗannan lokuta, yana da mahimmanci a tallafa wa iyayenmu maza da mata, bisa ga ƙa’idodin Omoluabi na kula da tsofaffi a cikin al’ummominmu.”

Dokta Alake ya kuma bayyana cewa, matakin da za a dauka nan gaba zai shafi sauran kungiyoyi masu rauni, da suka hada da zawarawa, marayu, nakasassu, da Ɗaliban manyan makarantu.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *