Fadar White House ta bayyana cewa akwai kungiyoyi 66 da Amurka za ta fita daga zama mamba a karkashin takardun da Trump ya sanya wa hannu, daga ciki akwai 35 da ba na MDD ba da kuma 31 a ke karkashin MDD.
Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wata takardar da ke nuna cewa za a janye Amurka daga ƙungiyoyi da dama na ƙasa da ƙasa, ciki har da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, in ji Fadar White House.
“A yau, Shugaba Donald J. Trump ya sanya hannu kan wata takardar da ke nuna cewa za a janye Amurka daga ƙungiyoyi 66 na ƙasa da ƙasa waɗanda ba sa ci gaba da biyan buƙatun Amurka, ciki har da: ƙungiyoyi 35 waɗanda ba na Majalisar Ɗinkin Duniya ba da kuma ƙungiyoyi 31 na Majalisar Ɗinkin Duniya,” in ji Fadar White House a ranar Laraba.
Fadar White House ba ta lissafo ƙungiyoyin ba amma ta ce suna yaɗa “manufofin sauyin yanayi masu tsauri, shugabancin duniya, da aƙidu waɗanda suka saɓa wa iko da tattalin arzikin Amurka.”
TRT Afrika
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t