Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu saka ran gyaruwar ƙasar a yayin da ake fuskantar kalubale, ya na mai bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya shawo kan su.
Ya yi wannan jawabi ne a jiya a karamar hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa, a lokacin kaddamar da kamfanin sarrafa waken siya da man sa, mallakar kungiyar CSS, da kuma bikin zagayowar ranar haihuwar Farfesa John Kennedy Opara, tsohon babban sakataren Hukumar Masu zuwa Bauta na Kiristoci ta Kasa (NCPC). .
Jonathan ya ce kasashen da ƴan Najeriya ke guduwa ai mutane ne su ka gina su, don haka akwai bukatar a dakatar da salon gudun hijirar da ake wa laƙabi da “Japa”.
Ya ce, “Ba kwa buƙatar yin Japa. Wadancan kasashen da ku ke guduwa mutane ne suka gina su. Dole ne muma mu gina kasar nan tare, mu saka hannun jari a cikinta domin matasa su samu ayyukan yi. Kada mu guje wa nauyin da ke kanmu. Wannan kasa tamu ce, kuma kada mu yi watsi da ita,” in ji Jonathan.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj