Fadar shugaban Najeriya ta janye jerin sunayen wadanda ta nada a yau juma’a, inda ta ce an tafka kura-kurai.
Sunday Dare, mashawarci na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan yada labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin X.
Sunday Dare, ya ƙarasa da cewa “sun lura da kurakurai da dama a wannan aiki sun kuma yi nadama.
Mashawarci na musamman ga shugaba Bola Tinubu, Dare ya fitar da jerin sunayen mutane 152 da aka naɗa da suka haɗa da mutanen yankin Arewa maso yamma mai fama da rashin tsaro,da wakilan kudu-maso-ƴamma su 29 da shugaban ƙasa ya naɗa.
Duk da cewa Dare ya bayyana kurakuran da ke cikin jerin sunayen, jaridar PREMIUM TIMES da ake wallafawa a Najeriya ta lura cewa ba a rasa sunayen wadanda aka nada ciki har da na shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
Yankin Kudu-maso-gabas shi ne a ƙasan jerin sunayen, inda aka naɗa mutane 16.
Ko da yake Dare bai bayyana dalilin da ya sa aka fitar da jerin sunayen ba, amma watakila bai rasa nasaba da zargin son zuciya da ake yi wa Shugaba Tinubu ba.
Wasu ƴan Najeriya sun sha nanata cewa shugaban ya fifita shiyyar sa, kudu maso yamma a naɗin da aka yi tun hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD