UEFA Ta Dauke Gasar Cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) Daga Rasha

Alfijr

Alfijr ta rawaito, kungiyar Kwallon Kafa ta Turai, a ranar Juma’a, ta dauke gasar cin kofin zakarun Turai ta maza ta 2021/2022 daga Rasha.

Alfijr

Hakan dai ya biyo bayan wani gagarumin taron kwamitin zartarwa na hukumar kwallon kafa ta UEFA da aka gudanar dangane da ta’azzarar yanayin tsaro a nahiyar Turai da Rasha ta mamaye kasar Ukraine.

Za a buga wasan karshe da aka shirya tun farko a Saint Petersburg a filin wasa na Faransa a ranar Asabar 28 ga Mayu, 2022, in ji UEFA a shafinta na yanar gizo.

Alfijr

Sanarwar ta kara da cewa, “UEFA na son mika godiyarta ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan goyon bayansa da kuma jajircewarsa na ganin cewa wasan da ya fi daukar hankalin kungiyoyin kwallon kafa na Turai ya koma Faransa a daidai lokacin da ake fama da rikici.

Tare da gwamnatin Faransa, UEFA za ta ba da cikakken goyon baya ga kokarin masu ruwa da tsaki da yawa don tabbatar da samar da ceto ga ‘yan wasan kwallon kafa da iyalansu a Ukraine da ke fuskantar mummunar wahala, lalata da kuma gudun hijira

Alfijr

“A taron na yau, kwamitin gudanarwa na UEFA ya yanke shawarar cewa Rasha kungiyoyin kasar Ukraine da ke fafatawa a gasar UEFA za a bukaci su buga wasanninsu na gida a wuraren da babu ruwansu har sai an samu zaman lafiya.

Slide Up
x