Wani Dan Takarar Majalisar Wakilai A APC Kano Ya Shiga Komar Jami an Tsaro, Bisa Zargin N13m

Alfijr ta rawaito Dan Takarar Majalisar Wakilai Na Jam’iyyar All Progressives Congress A Rano, Kibiya, Bunkure, a Kano, Dr Aliyi Musa Aliyu, ya fada komar jami an tsoro kan badakalar sama da Naira miliyan 13. .

Lamarin ya fara ne yayin da wani Rabiu Saidu ya kai karar Aliyu tsohon Darakta Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ga Caji Ofis din ƴan sandan na Dala.

Alfijr Labarai

Wata majiya ta shaida wa wannan jarida cewa ‘yan sanda sun kamal wani abokinsa Ghali Ibrahim.

A cikin takardar karar da wanda abin ya shafa, Rabiu Saidu, a ofishin ‘yan sanda, Aliyu tare da Dakta Ghali Ibrahim, sun karbo masa kudi har naira miliyan 13 domin gudanar da kasuwanci sama da watanni 5, tun daga lokacin bai amsa kiransa ba kuma bai yi magana ba.

Bayan alkawari a kan mayar da kudin, bayan kiraye-kiraye da sakonni da ya aika a wayoyinsa na hannu yana kin sauraro.

Alfijr Labarai

Wakilinmu ya yi kokarin kiran lambobin wayar Dr. Aliyu tun ranar Asabar din da ta gabata har zuwa daren Litinin amma layukan wayar a kashe.

Haka kuma duk kokarin da ‘yan sandan suka yi na cafke Dakta Aliyu ya ci tura domin ya kashe wayar sama da mako guda yana gudun Hijira.

sai dai wata majiya ta tabbatar da ranar Litinin din da ta gabata cewa rundunar ‘yan sanda ta Dala za ta mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka a ranar Talata na hukumar ƴan sanda ta jihar Kano

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Solacebase

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *