Wani Hadarin Kwale Kwale Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 26

Alfijr

Alfijr ta rawaito Mutane 26 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da ake ci gaba da neman wani jirgin ruwa a kogin Shagari da ke karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Shugaban karamar hukumar Shagari, Alhaji Aliyu Dantani, wanda ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hatsarin a ranar Laraba a Sokoto, ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

Dantani ya ce daga cikin gawarwakin mutane 26 da aka gano, 21 mata ne yayin da biyar kuma kananan yara, ya kara da cewa ana ci gaba da aikin ceto i zuwa yanzu

Alfijr

Shugaban karamar hukumar, ya ce ba a iya tantance hakikanin adadin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen.

A cewarsa, a halin yanzu ma’aikatan ruwa na cikin gida suna cikin kogin don ganin yadda za a kwato gawarwaki ko kuma ceto wadanda suka tsira.

Kamar yadda Solacebase ta wallafa