Kotun Daukaka Kara ta Bada Umarnin Sake Gurfanar da A. A Zaura Bisa Laifin Zambar Dalar Amurka miliyan 1,320,000

Alfijr

Alfijr ta rawaito kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin sake shari’ar damfarar dan takarar gwamnan jihar Kano a APC Abdulsalam Sale Abdulkadrim Zaura.

A wani mataki na bai daya a ranar Larabar da ta gabata, kwamitin alkalan kotun uku ya yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke tun farko, wadda ta sallami dan kasuwan tare da wanke shi.

Hukuncin wanda mai shari’a Abdullahi Bayero ya yanke, ya kuma bayar da umarnin gudanar da shari’ar wanda ake kara a wata kotu banda ta mai shari’a Allagia.

Alfijr

Zaura, wanda aka fi sani da A A Zaura a cikin harkar siyasa, hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da shi gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyar.

An zarge shi da damfarar wani dan kasar Kuwaiti ta hanyar karbar kudi dalar Amurka miliyan 1,320,000 (Dala miliyan daya da dari uku da ashirin) bisa zargin cewa yana sana’ar gine-gine a Dubai, Kuwait da sauran kasashen Larabawa.

Alfijr

A ranar 9 ga watan Yuni, 2020, babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari’a Allagoa ta samu wanda ake kara ba shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen da ake tuhumarsa da shi, ta kuma sallame shi.

Babban abin da ake ta cece-kuce da shi a kotun daukaka kara shi ne wanda ake tuhumar bai halarta ba a lokacin da aka yanke hukunci kuma an sallame shi. bisa wasu hukunce-hukuncen kotun koli, an yanke hukuncin cewa wanda ake tuhuma dole ne ya kasance a gaban kotu a duk lokacin da ake shari’ar da ake yi masa ciki har da yanke hukunci.

Alfijr

Dangane da haka ne kotun daukaka kara ta samu damar cigaba da shari ar, kuma ta amince da hakan.

“Bayan an tantance batun don goyon bayan wanda ya shigar da kara, a dabi’ance karar ta yi nasara.

An soke hukuncin da karamar kotu mai lamba FHCK/CR2018/FRN ta yanke kan Abdulsalam Sale Abdulkarim wanda aka yanke ranar 9 ga watan Yuni, 2020.”

In ji kotun daukaka kara.

Slide Up
x